MA'ANAR BORI
Bori wata al'ada, kuma sana'a ce ta maguzanci wadda Hausawa ke gudanarwa tun kafin zuwan addinin musulunci kasar Hausa har zuwa yanzu bayan zuwan musulunci wadda 'yan bori ke biya wa aljannu bukatunsu, su kuma su biya wa mai yin borin tasa bukatar wadda ita ce hanyar bayar da maganin gargajiyar Hausawa.(Dawud 2008).
Bori wata al'ada ce ta bautawa iskokai wadanda ke ganinmu amma mu ba mu ganinsu, wadda Hausawa ke amfani da ita wajen neman waraka ta wadansu cututtuka ko neman biyan waya bukata(Sani 2009)·
A takaice dai za a iya cewa bori tsohuwar al'adar Hausawa ce wadda ake amfani da iskoki tare da yin amfani da wadansu magunguna irin su turaren magani, sauyoyi da turare da manufar biyan waya bukata ko bayar da maganin wani ciwo kamar ciwan iskoki, maganin shan inna da maganin farfadiya.
Mustapha Salmanu kofar Sauri Katsina 08037675446

Comments
Post a Comment