TARIHIN SANA’AR BORI
Tarihi ya nuna cewa shi dai bori shi ne imanin Bahaushe na asali, domin kuwa kowace al’umma idan aka bi tushe ko asalinta za a tarar tana da wata hanyar da ta ke bi don yarda da wani abu mai girma wanda suka dogarar da rayuwarsu akansa. Tun can asali ma a kan samu wadansu al’ummomi da suke bautar gumaka ko iskoki ko taurari ko wuta da sauransu.
Haka kuma tarihi ya nuna cewa kafin shigowar wasu bakin al’ummomi a kasar Hausa, Hausawa suna da addininsu na gargajiya.A sakamakon irin nazarce-nazarce da aka yi a baya dayawa daga cikin masana na nuna cewa tarihin bori shi ne addinin gargajiya na Hausawa kai har ma da wasu wadanda ba Hausawa ba.
A wani bincike da na yi na samu wani littafi mai suna ‘Dangantakar Al’ada Da Addini’ wanda a cikin littafin aka nuna irin dangantakar da ke tsakanin al’ada da addini, domin a cikin littafin an nuna cewar daya daga cikin addinin gargajiya na Hausawa shi ne Bori wato bautar iskokai.
Bori tsohuwar al’ada ce wurin Hausawa tun fil’azal, abin day a sa aka ce haka kuwa shi ne sun fara al’adun ne tun lokacin das u ke duk maguzawa ne kuma har yanzu da mafi yawancinsu musulmai ne bas u daina wannan al’adar ba.
A jawabin Dakta Alhaji Yusuf Mai tama Sule (Dan Masanin Kano 1973) wanda sashen binciken Harsunan Najeriya Na Jami’ar Bayero Kano ya yi bayani a kan tarihin bori cewa ‘Duk inda jama’a ko kabilu ko jinsi suka taru to lallai a samu wani addini wanda a cikinsa ne mutane ke neman ceto ko dogaro ko ilhama,kazalika su kan yi amfani da wannan addini domin neman sanin gaibi ko neman sauki da waraka daga wasu cututtuka. Kuma wannan yarda haka ta keg a wadanda suke bin addinin Allah daya ko bautawa wanin Allah, wannan yana yi mana bayani cewa harkar bori mutane sun danganta ta da Allah wanda daga baya ya zamo kamar aljannu kawai ake bauta ma wa tare da tsafe-tsafe.
Hausawa sun dauka cewa banda mutane, duniya na cike da wasu boyayyun halittu ma su dabi’a irin ta mutane. Saboda haka su ke kiransu ‘mutanen boye’. Kamar yadda aka fahimta su mutanen boye su ne wadanda bayan zuwan addinin musulunci ake kiransu aljannu ko iskokai kamar yadda Kur’ani ya bayyana a cikin sura ta 72 aya ta 1 zuwa ta 16,
A takaice wannan shi ne tarihin al’adar bori a dan karamin bincike na. Da fatan za a sanar da ni idan an ga wani kuskure a cikin rubutun.
Naku a kullum Mustapha Salmanu Kofar Sauri Katsina 08037675446 mustaphasalmanu00@gmail.com

Comments
Post a Comment