NAZARIN DA SHARHIN LITTAFIN WASAN KWAIKWAYO (KULBA NA BARNA...)
.
-MAWALLAFI: UMARU DANJUMA KATSINA (KASAGI)
SHEKARAR BUGAWA: 1979
SABUNTAWA: 1985; 2004; 2006; 2007
ISBN: 978-978-169-245-1
GABATARWA:
'KULBA NA BARNA...' littafin wasan kwaikwayo ne wanda ke kunshe da labarin wata yarinya 'yar makaranta mai suna Zaliha. Mahaifinta, Malam Bankami, mutumin kauye ne, ya rasu ya bar ta riko a hannun Kawunta da ke zaune a wani babban gari. Kawun nata, Malam Inuwa, ya so cika wasiyyar Mahaifin Zaliha na aurar da ita da zarar ta kammala makarantar firamare, har ba shi ma fatar ta ci jarabawar shiga babbar makaranta, kamar yadda yake cewa,
.
''Ai da ma a cikin wasiyyar da ya bari, ya ce don Allah don Annabi idan Zaliha ta isa aure, in yi mata. Ya ce in aurar da ita ga duk wanda za ta samu zaman lafiya. Don haka ma nake fatar ka da Allah sa ta ci jarabawar nan ta zuwa makarantar 'yan mata.''
.
Tuni dai har Malam Inuwa ya gama maganar auren Zaliha da iyayen saurayin da za ta aura mai suna Dantakarda. To sai ga shi kuma ta ci jarabawar shiga babbar makaranta, hakan ya sa gwamnati ta matsa kaimi ala-dole sai ta ci gaba da karatu. A nan ma ga yadda Malam Inuwa ke cewa,
.
''To ni abinda muka shawarta da sauran dangina da abokan arzika shi ne, so muka yi ka da ta je makaranta, to amma hukuma ta fi karfinmu, ta ce dole ta je makaranta, saboda haka babu yadda za mu yi, mu ma tilas muka yarda ta tafi din.''
.
Bayan ta shiga makarantar kwanan da ke garinsu ta 'yan mata, sai ga shi wani Alhaji Ruwan Ido da suka hadu da shi a gari yana zuwa har makarantar yana fita da ita, ta hanyar saye maigadin makarantar da 'yan kudade kalilan. Daga karshe dai ya yaudare ta, tare da taimakon wani babambadensa, Zumudi, wai Alhaji zai aure ta. Ga yadda Zumudin ke fadi mata,
.
''... Ni tun kwanaki ya dame ni wai in samo mishi yarinya 'yar makaranta wacce za shi aura. Ni kuma na duba tsai duk unguwarmu ba wacce ta dace da shi sai ke...''
.
Da ta ji haka, sai ta aikawa saurayinta (Dantakarda) da wasika cewar ya nemi wata ya yi aure, ita fa ta zama sai mai rabo, har take cewa a cikin wasikar, ''Ni yanzu na zama indifanda, na samu 'yancin kaina, aurena sai mai rabo...'' Daga haka sai wata mata, Dela, ta ba shi 'yar dan uwanta mai suna, Amarya, ya aura.
.
Tafiya dai ta yi tafiya, Alhaji Ruwan Ido da Zumudi suka yi ta rudar Zaliha har ta ba shi dama ya yi mata ciki; sanadin haka aka kore ta daga makarantarsu, ta dawo gida da cikin wata d'aya. Gudun abin kunya ya sanya Zaliha barin garinsu, ta tafi wani gari ta ci gaba da zaman kanta (karuwanci). A can ne kuma ta hadu da wani tsohon saurayinta, Danlondon, inda ya gargade ta da ta koma gida shi zai aure ta. Hakan kuwa aka yi, ya mai do ta gida aka daura musu aure.
.
GABATAR DA JIGON WASAN KULBA NA BARNA...:
Takamaimai ba za a iya fitar da wani jigo a cikin wannan wasa a ce shi ne babban jigonsa ba, sai dai a yi kirdado a fadi, abinda ya yi saura kuma sai idan an yi sharhin jigogin ne kowa zai yi hasashe ya fadi nashi ra'ayi game da babban jigon wasan ko kuma dai idan mutum ya karanta littafin da niyyar nazari a kan sa. Amma duk da yake haka, kowa dai ya san jigo shi ne manufa ko makasudin da ya sa aka yi wani aikin adabi, to shi ma mawallafin wannan wasa ba zai rasa manufar da yake son cimmawa ba.
.
A yadda na nazarci wasan Kulba Na Barna, ina tsammanin jigo mafi muhimmanci shi ne yin GARGADI ga masu halin KWADAYI. Da ma dai kowa ya san Kwadayi mabudin wahala ne, kuma duk wanda ya hau motarshi, to za ta sauke shi ne a tashar wulakanci. Bayan wannan gargadi, wasan dai na kunshe da wasu jigogi kama daga TAUSAYAWA da DUNIYANCI da YAUDARA da SOYAYYA da ZUMUNTA da sauransu.
.
WARWARAR JIGOGI:
Bari mu fara da jigon KWADAYI, wanda shi ne ya jaza afkawar da Zaliha ta yi cikin halin ni-'ya-su. Domin fito da wannan jigo a tashin farko, ga tsakuren hirar da Alhaji Ruwan Ido ya yi da Zumudi, ranar farko da suka ga Zaliha na wucewa ta kofar gidan na Alhaji,
.
Zumudi: To Alhaji in dan abotaka kake son waccan yarinya, ni ina ganin fuskarta lallai ta yi tsiwa.
Alhaji: Haba Zumudi! Mace ai kamar rakumi take, duk inda ka nufa da ita yarda za ta yi. Da farko zan yi ta mata kyauta ne. Na san dai duk wanda ake yi wa kyauta yana karba, komai tsiwarsa watarana ya bari.
Zumudi: Yauwa Alhaji ashe ka gane. Ai wannan sha'ani ya zo gidan sauki tun da 'yar makaranta ce. Na kuwa lura 'yan makaranta son kudi ke gare su. (Shafi na 11)
.
Bayan wannan tattaunawa, sai a can gaba Alhaji ya fara jarraba Zaliha domin ya gane shin ko tana da kwadayi? A inda suka kira ta shi da Zumudi da za ta wuce ta gabansu, bayan sun dan taba hira da ita, sai ta ce za ta wuce zuwa gida. Nan Alhaji ya fara yi mata kyauta,
.
Alhaji: .... Ke yarinya karbi in ba ki Naira biyar ko biskit ki saya domin na san abincin makaranta ba ya isar ku. (Shafi na 25).
.
Zaliha dai ta karba har da godiya. Ta dalilin haka ya samu damar yi mata tambayoyi game da sirrin zuwa ziyarar makarantarsu, ta kuma bayyana mishi komai filla-filla, tare da cikakken sunanta ko da zai je nemanta.
.
Alhaji dai ya sha alwashin zuwa makarantar su Zaliha da zarar sun koma, sai dai Zumudi ya kawo hanzari da cewar akwai maigadi, kuma ba yadda za a yi ya bar su, su shiga. Nan ma jigon kwadayi ya bayyana, inda Alhaji ke cewa:
.
Alhaji: Ahaf! Maigadin da zan saya. Yanzu da na ba shi Naira guda, sai ya bar ni in wuce... (Shafi na 26).
.
Kawun Zaliha, Malam Inuwa, na yi mata gargadi duk lokacin da za ta koma makaranta. A cikin gargadin yana cewa,
.
M. Inuwa: ... Kuma don Allah don Annabi a rinka karatu, ban da kuma kwadayi! (Shafi na 29).
.
Bayan an koma makaranta, Alhaji da Zumudi sun samu zarafin zuwa makarantar ta su Zaliha. Sai dai kamar yadda Zumudi ya fadi, maigadi ya yi turjiya; sai da kyar suka shawo kansa sannan suka shiga. Sun samu ganin Zaliha, har Alhaji ya yi mata kyauta, tare da alkawarin wanshekare za su dawo su je da ita kanti a yi mata sayayya. Hakan ya sa ta kara sakin jiki da su Alhaji. Ko a nan ma kwadayi ne ya jaza hakan.
.
Kamar yadda Alhaji ya ce a baya, zai saye maigadi, hakan kuwa aka yi, inda bayan sun zo fita ne Alhajin ya kira maigadin,
.
Alhaji: Karbi nan Baba Maigadi, ga Naira goma, amma don Allah ka yi hakuri. (Shafi na 36).
.
Da Alhaji ya yi mishi wannan kyauta, sai kuma suka ce mishi gobe ma za su dawo, nan da nan ya ba su dama, inda ya ce,
.
Maigadi: To ai babu komai. Tun da shike na ji an ce Baturiya za ta kai wata ziyara a makarantar 'yan mata wacce take Dogon Dutse. (Shafi na 37).
.
Zumudi dai ya fito da wannan jigo a fili tinya. Bayan sun dawo daga makarantar ne suna hira da Alhaji a dakin hutawarshi, sai ya ce,
.
Zumudi: 'Yan matan yanzu ai samun su ba wuya. In dai kana da mota da kuma wasu kudi a aljihunka, ai Alhamdulillahi! (Shafi na 37)
.
A karshen karshe dai kwadayi ya jefa Zaliha cikin mawuyacin hali, wanda ya kai ta ga yin cikin shege da kuma afkawa mummunar hanyar karuwanci.
.
JIGON TAUSAYAWA:
Hakika a wannan wasa akwai abubuwan tausayawa da suka faru ba kadan ba. Hatta ga Zaliha, wacce ta kasance marainiya (ba uwa ba uba), amma ta tsinci kan ta cikin halin kankanci ba karamin abin tausayi ba ne. Haka ma ga
marikinta wanda ke bakin kokarinsa wajen ganin ya cika wasiyyar yayansa, halin da Zaliha ta sanya shi abin a tausaya ne shi ma. Ga kuma masoyin Zaliha wanda ta yi masa butulci, da zarar an tuna da soyayya, dole ne shi ma a tausaya mishi.
.
JIGON YAUDARA:
Wannan jigo shi ma ya dauki kaso mai tsoka a wannan wasa, ganin irin yadda Alhaji Ruwan Ido da Zumudi suka shirya wa Zaliha gadar zare ta hanyar rudarta da suka yi har Alhaji ya yi mata ciki. Babbar yaudarar da suka yi amfani da ita ba ta wuce yadda suka je wa Zaliha a sifa ta kamala, suka kuma ce sun je ne a matsayin
masoya; wai Alhaji zai aure ta ne. Kuma tsagwaron yaudara ne.
.
JIGON SOYAYYA:
Yadda Zaliha suka gudanar da soyayyarsu ita da masoyinta, Dantakarda ba karamin abin sha'awa ba ne. Ga kuma soyayyar da Dantakarda ya rinka nuna wa matar da ya aura, Amarya, bayan da Zaliha ta ce ba ta aurenshi. Wannan shi ne zai dauki jigon soyayya a wannan wasa. Bari in dan tsakuro mana kadan daga hirar Dantakarda da Matarshi:
.
Dantakarda: Amarya! Ina Amaryar take ne?
Amarya: Sannu da zuwa Malam.
Dantakarda: Yauwa sannu kadai. Ina abinci?
Amarya: Malam ba ka ko hutawa tukuna?
Dantakarda: To na ji. Dauko ludo din ki mu dan taba.
Amarya: Ni dai Malam ina son yin ludo da kai amma rinto ke gare ka. In ka san za ka yi mini rinto ba zanyi ba.
Dantakarda: Allah yau ba zan yi rigima ba. Idan kika kashe mini d'ana kin kashe ke nan.
Amarya: To amma ni ke da danja, ni kuma zan fara kadawa.
Dantakarda: Na yarda!
.
JIGON DUNIYANCI:
Alhaji: Af to kuma za ka tafi ba ka ba ni labarin yadda kuka kare da mutuniyarka ba.
Zumudi: Wace ce?
Alhaji: Zo mana in rada maka.
Zumudi: A'a ai ba kowa kusa da mu, mu biyu ne kawai ka fadi mini in za ka fadi mini. (Shafi na 11).
.
Ko a wannan hirar kadai na tsaya, to jigon duniyanci ya fito karara a wannan wasa. Bari mu dakata a nan game da nazarin jigogi, mu durfafi Zubi Da Tsarin littafin wasan mu ga abinda ya k'unsa.
.
ZUBI DA TSARIN WASAN KULBA NA BARNA.
Tun da farko dai mawallafin wasan Kulba Na Barna ya yi zubin wasan ne ta hanyar kashi-kashi; inda wasan ya kunshi kashe-kashe guda uku. Bayan wannan kashe-kashe ne sai kuma ya yi amfani da tsarin shiga-shiga tare da gabatarwa a mafi yawancin kowace shiga da za a yi. Kashi na farko na da shiga biyar, a shiga ta daya da ta biyar su ne ba a yi gabatarwa ba. Ga yadda tsarin yake a kashin farko:
Shiga Ta Daya- A Gidan Malam Inuwa.
Shiga Ta Biyu- A Gidan Goggo.
Shiga Ta Uku- A Zauren Malam Inuwa.
Shiga Ta Hudu- A Sabon Gidan Alhaji (Kofar Gida).
Shiga Ta Biyar- A Gidan Kilima.
.
Sai Kashi na Biyu, wanda ya kunshi shiga guda hudu da gabatarwa a kowace shiga. Tsarin da wuraren shigarsa sun kasance ne kamar haka:
Shiga Ta Daya- A Gidan Malam Inuwa.
Shiga Ta Biyu- A Dakin Dantakarda.
Shiga Ta Uku- A Gidan Goggo.
Shiga Ta Hudu- A Kofar Gidan Alhaji.
.
Kashi Na Uku, wanda kuma shi ne kashi na karshe a wasan yana da shiga-shiga har goma sha biyu da gabatarwa guda goma:
Shiga Ta Farko- A Gidan Goggo.
Shiga Ta Biyu- A Gidan Malam Inuwa.
Shiga Ta Uku- A Bakin Kofar Makaranta.
Shiga Ta Hudu- A Dakin Hutawar Alhaji.
Shiga Ta Biyar- A Makaranta.
Shiga Ta Shida- A Dakin Alhaji.
Shiga Ta Bakwai- (Ba a kawo ta ba).
Shiga Ta Takwas- A Gidan Goggo.
Shiga Ta Tara- (Ba a bayyana wuri ba).
Shiga Ta Goma- (Ba a bayyana wuri ba).
Shiga Ta Goma Sha Daya- (Ba a bayyana wuri ba.)
Shiga Ta Goma Sha Biyu- (Ba a bayyana wuri ba.)
.
A tsarin wasan dai an yi amfani da baka biyu ( ) wajen shigar da motsawar taurari da wakanar ayyukansu, misali a ce,
(Shiga) ko (Fita) ko (Gaisuwa) da makantansu.
.
Littafin wasan Kulba Na Barna akwai hotuna a wadansu wurare da ke nuna aukuwar motsin taurari, kodayake ba a saka hotunan a ainahin wuraren da magana ke wakana ba. Misali, a kashi na biyu, shiga ta hudu, inda Alhaji da Zumudi ke hira a kofar gidan na Alhaji, sai aka yi hoton Zaliha da Alhaji ne a daki rungume da juna.
.
SALO DA SARRAFA HARSHE.
Salon wasan Kulba Na Barna sassauka ne sosai. An ja zaren wasan daki-daki, daga farko har karshe; ba wani tafiyar kura ko dai wani salo na daban mai rikitarwa. Salo ne dai sassauka kuma mikakke.
.
Ta bangaren Sarrafa Harshe ma wasan bai dauki kaso mai tsoka ba, illa a wadansu 'yan wurare da taurarin suka yi amfani da azancin ko karin maganganu. Misali,
Kilima:... Wash! Tsufa labari, mutuwa karar kwana...(Shafi na 17).
Zumudi:... Kai dai a dun ga zuwa rafi, na san watarana an fasa tulu...(Shafi na 38).
Alhaji: Faduwar gaba, asarar namiji. (Shafi na 54).
Zumudi:... Ka gaya masa, hawainiyarsa ta kiyayi ramata! (Shafi na 55). Kodayake hatta sunan wasan ma (Kulba Na Barna) shi ma azancin magana ce ta Bahaushe.
.
NAZARIN TAURARI.
A wannan wasa za a iya cewa Zaliha ita ce babbar tauraruwar wasan, ta yi magana kusan sau 96. Bayan haka ma, ita ce ginshikin wasan; ita aka fi ba muhimmanci. Akwai Danlondon, wanda shi tauraro ne mai walkiya; tun da ya yi magana a kashin farko, bai sake cewa komai ba sai a kashi na karshe ya sake bayyana. Taurarin wasan dai su goma sha tara ne baki dayansu, ga jerinsu:
Zaliha
Malam Inuwa
Mai-Nakada
Alhaji Ruwan Ido
Zumudi
Kilima
Dantakarda
Goggo
Akawu
Danlondon
Dela
Baba Maigadi
Amarya
Gyartai
Yarinya
Yaro
Fulani
Magajiya
Yan Matan Amarya
.
TAKAITACCEN TARIHIN MAWALLAFIN WASAN 'KULBA NA BARNA...'
.
An haifi Alhaji Umaru Danjuma Kasagi a shekarar 1948 a cikin birnin Katsina. Ya yi karatun firamare a tsakanin 1960 da 1965. Daga ya ci gaba zuwa Provincial Secondary school Katsina, 1966-1972. Ya fara aiki a 'North Central state Arts Council'. Bai dade a nan ba ya tafi kasar Ingila don ci gaba da karatunsa, wanda ya shafi aikin talabijin da wasan kwaikwayo a wajajen 1975.
.
Alhaji Umar Danjuma ya dawo Nijeriya a shekarar 1980 inda ya kama aiki da Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya, a Cibiyar Nazarin Al'adun Nijeriya da ke Jami'ar. Ya aje wannan aiki nasa a shekarar 1992.
.
Alhaji Umar Danjuma Katsina, ya samo sunan Kasagi ne daga wani mashahurin wasan kwaikwayo wanda Gidan Talabijin Na Kasa ya dauki nauyinsa, a shekarar 1980, a zamanin mulkin Shagari. Wasa ne da ke jan hankalin matasan da ke barin karkara zuwa birane. Yana da kirarin da ake yi mishi a wannan wasa, "Kasagi Na Halima, abokin fada ga naka!" Ma'anar "Kasagi" dai shi ne mutum mayawaci, wanda bai san ina ya ba kai ba.

Comments
Post a Comment