Skip to main content

Posts

Showing posts from December, 2018
TARIHIN SANA’AR BORI Tarihi ya nuna cewa shi dai bori shi ne imanin Bahaushe na asali, domin kuwa kowace al’umma idan aka bi tushe ko asalinta za a tarar tana da wata hanyar da ta ke bi  don yarda da wani abu mai girma wanda suka dogarar da rayuwarsu akansa. Tun can asali ma a kan samu wadansu al’ummomi da suke bautar gumaka ko iskoki ko taurari ko wuta da sauransu. Haka kuma tarihi ya nuna cewa kafin shigowar wasu bakin al’ummomi a kasar Hausa, Hausawa suna da addininsu na gargajiya.A sakamakon irin nazarce-nazarce da aka yi a baya dayawa daga cikin masana na nuna cewa tarihin bori shi ne addinin gargajiya na Hausawa kai har ma da wasu wadanda ba Hausawa ba. A wani bincike da na yi na samu wani littafi mai suna ‘Dangantakar Al’ada Da Addini’   wanda a cikin littafin aka nuna irin dangantakar da ke tsakanin al’ada da addini, domin a cikin littafin an nuna cewar daya daga cikin addinin gargajiya na Hausawa shi ne Bori wato bautar iskokai. Bori tsohuwar al’ada ce w...
        MA'ANAR BORI    Bori wata al'ada, kuma sana'a ce ta maguzanci wadda Hausawa ke gudanarwa tun kafin zuwan addinin musulunci kasar Hausa har zuwa yanzu bayan zuwan musulunci wadda 'yan bori ke biya wa aljannu bukatunsu, su kuma su biya wa mai yin borin tasa bukatar wadda ita ce hanyar bayar da maganin gargajiyar Hausawa.(Dawud 2008).    Bori wata al'ada ce ta bautawa iskokai wadanda ke ganinmu amma mu ba mu ganinsu, wadda Hausawa ke amfani da ita wajen neman waraka ta wadansu cututtuka ko neman biyan waya bukata(Sani 2009)·   A takaice dai za a iya cewa bori tsohuwar al'adar Hausawa ce wadda ake amfani da iskoki tare da yin amfani da wadansu magunguna irin su turaren magani,  sauyoyi da turare da manufar biyan waya bukata ko bayar da maganin wani ciwo kamar ciwan iskoki, maganin shan inna da maganin farfadiya.    Mustapha Salmanu kofar Sauri Katsina 08037675446  

Zaman Gandu a al'adar Malam Bahaushe

Zaman iyali ya kumshi zama ne na mutum da matarsa ko matansa da 'ya'yansa. A tsarin zaman Hausawa na gargajiya, magidanta suna bin tsarin zaman gandu ne wanda yakan kasance zaman babban gida da ya kunshi sashin maigida, da sashin kannensa da 'ya'yansa, su ma wasu daga cikinsu magidanta ne, watau suna da nasu iyalin. Saboda haka shi kansa gandun zama ne na iyalin babban maigida, amma a cikin gandun akwai kananan masu gida da iyalansu. Wato kenan bisa ga al'ada, iyalin Bahaushe ba kurum sun kunshi matansa da 'ya'yansa ba ne, a'a, har ma da duk wani wanda yake karkashin ikonsa, ko sun hada dangantaka ta jini, misali kamar 'yanuwansa, da sauran danginsa da 'ya'yansu, ko kuma ba su hada dangantaka ta jini ba, misali matan 'ya'yansa, da barori ko yaran gida, da 'yan aikin gida. A tsarin zaman gandu duk iyalansa ne. Shi babban maigida, wanda akan kira da Babangida, ya zama uba ga wasu mutanen gida kuma kaka ga wadansu. Tsarin zaman ...