AL'ADAR ZANCEN K'ARSHE Masu iya magana kan ce 'darajar galan marfinsa haka kuma duk darajar girman tuwo sai an sa masa miya'. Sannan masana (addini da boko) sun tabbatar mana da cewar duk al'ummar da ta yada al'adarta, ko shakka babu wannan al'umma ta shiga garari (rud'ani). 'Zancen 'karshe' al'ada ce wadda ake gudanarwa a wani yanki na garin Katsina. Wannan al'adar na d'aya daga cikin al'adun auren Hausawa a wannan yanki. Ana gudanar da wannan al'ada ne a ranar daren daurin aure; wato ana gobe za a d'aura aure kenan, sannan ana yin zancen 'karshe ne da daddare. Yadda ake gudanar da wannan al'ada shi ne; A ranar daren daurin aure da safe zuwa marece za a sanar da abokanin ango inda za a had'u domin zancen 'karshe, ita ma ta 'bangaren amarya za a sanar da 'kawaye wurin da za a had'u domin zancen 'karshe. Kafin lokacin ya yi abokanin ango za su tanadi kayayyakin ma'kulashe kama...