Skip to main content

TARIHIN HASSAN SARKIN DOGARAI KANO

Hassan Adamu, da aka fi sani da Hassan sarkin Dogarai, shine sarkin Dogarai na uku da marigayi sarkin Kano, Ado Bayero ya nada a mastayin shugaban dogaran sarki a shekarar 1990.


Kafin nadin Hassan a matsayin sarkin dogaran fadar Kano, Marigayi Ado ya nada wasu mutane biyu a baya; Dan-Wudil da Adamu, kuma bayan mutuwar Adamu ne aka nada Hassan, sannan shi ma bayan mutuwarsa aka nada sarkin Dogarai na yanzu, Danbala.


Sai dai sabanin sarkin dogarai Adamu da Dan-Wudil, Hassan ba bafade ba ne. Asalinsa direba ne da ke sana’ar tuka mota kafin daga baya ya zama hadimi ga galadiman Kano, Marigayi Tijjani Hashim, mutumin da ya fara nada shi a matsayin shamakinsa kuma ya zama silar shigar sa cikin fadar Kano.

A shekarar 1990 ne, bayan mutuwar sarkin Dogarai Dan-Wudil, Marigayi Hashim ya roki sarkin Kano Ado alfarmar ya nada Hassan a matsayin sarkin Dogarai saboda tsananin biyayyarsa da kuma jarumtarsa, sannan ga soyayya da ya ke nunawa ga sarkin.

Marigayi Hassan na zaune ne da iyalinsa a unguwar Sagagi, kusa da gidan mahaifiyar Ado Bayero, kafin daga bisani ya koma unguwar gidan sarkin Dogarai da ke unguwar Dogarai, daf da gidan sarkin Kano.


Hassan ya yi shura a cikin sarakunan Dogaran Kano saboda karfi da jarumta da kuma tsananin biyayyarsa ga sarkin Kano Ado.


Hassan sharcecen mutum ne, saboda girma da tsayinsa har kirari ake yi masa da Bishiya.


Wani dan asalin unguwar Dogarai, Ibrahim Mu’azzam Sadauki, da ya san marigayi Hassan, yace "Marigayi Hassan ya fara haduwa ne da shahararren mawakin Hausa, Mamman Shata, yayin da ya ke sana’ar sa ta tuka mota. Bayan Hassan ya zama sarkin Dogarai ne, Shata ya rera masa wakar “Hassan sarkin Dogarai”, wakar da ta kara daukaka sunansa a Duniya".


Yanzu haka iyalan Hassan sun koma gidansa dake unguwar Sagagi inda suka cigaba da rayuwa bayan mutuwar mahaifinsu.

Allah ya jikansa da rahama,amiin

Comments

Popular posts from this blog

NAZARIN LITTAFIN KUL'BA NA 'BARNA NA UMARU 'DANJUMA KATSINA

NAZARIN DA SHARHIN LITTAFIN WASAN KWAIKWAYO (KULBA NA BARNA...) . -MAWALLAFI: UMARU DANJUMA KATSINA (KASAGI) SHEKARAR BUGAWA: 1979 SABUNTAWA: 1985; 2004; 2006; 2007 ISBN: 978-978-169-245-1 GABATARWA: 'KULBA NA BARNA...' littafin wasan kwaikwayo ne wanda ke kunshe da labarin wata yarinya 'yar makaranta mai suna Zaliha. Mahaifinta, Malam Bankami, mutumin kauye ne, ya rasu ya bar ta riko a hannun Kawunta da ke zaune a wani babban gari. Kawun nata, Malam Inuwa, ya so cika wasiyyar Mahaifin Zaliha na aurar da ita da zarar ta kammala makarantar firamare, har ba shi ma fatar ta ci jarabawar shiga babbar makaranta, kamar yadda yake cewa, . ''Ai da ma a cikin wasiyyar da ya bari, ya ce don Allah don Annabi idan Zaliha ta isa aure, in yi mata. Ya ce in aurar da ita ga duk wanda za ta samu zaman lafiya. Don haka ma nake fatar ka da Allah sa ta ci jarabawar nan ta zuwa makarantar 'yan mata.'' . Tuni dai har Malam Inuwa ya gama maganar auren Zaliha da iya...

ZANCEN KARSHE

AL'ADAR ZANCEN K'ARSHE    Masu iya magana kan ce 'darajar galan marfinsa haka kuma duk darajar girman tuwo sai an sa masa miya'. Sannan masana (addini da boko) sun tabbatar mana da cewar duk al'ummar da ta yada al'adarta, ko shakka babu wannan al'umma ta shiga garari (rud'ani).  'Zancen 'karshe' al'ada ce wadda ake gudanarwa a wani yanki na garin Katsina. Wannan al'adar na d'aya daga cikin al'adun auren Hausawa a wannan yanki. Ana gudanar da wannan al'ada ne a ranar daren daurin aure; wato ana gobe za a d'aura aure kenan, sannan ana yin zancen 'karshe ne da daddare. Yadda ake gudanar da wannan al'ada shi ne; A ranar daren daurin aure da safe zuwa marece za a sanar da abokanin ango inda za a had'u domin zancen 'karshe, ita ma ta 'bangaren amarya za a sanar da 'kawaye wurin da za a had'u domin zancen 'karshe. Kafin lokacin ya yi abokanin ango za su tanadi kayayyakin ma'kulashe kama...
TARIHIN SANA’AR BORI Tarihi ya nuna cewa shi dai bori shi ne imanin Bahaushe na asali, domin kuwa kowace al’umma idan aka bi tushe ko asalinta za a tarar tana da wata hanyar da ta ke bi  don yarda da wani abu mai girma wanda suka dogarar da rayuwarsu akansa. Tun can asali ma a kan samu wadansu al’ummomi da suke bautar gumaka ko iskoki ko taurari ko wuta da sauransu. Haka kuma tarihi ya nuna cewa kafin shigowar wasu bakin al’ummomi a kasar Hausa, Hausawa suna da addininsu na gargajiya.A sakamakon irin nazarce-nazarce da aka yi a baya dayawa daga cikin masana na nuna cewa tarihin bori shi ne addinin gargajiya na Hausawa kai har ma da wasu wadanda ba Hausawa ba. A wani bincike da na yi na samu wani littafi mai suna ‘Dangantakar Al’ada Da Addini’   wanda a cikin littafin aka nuna irin dangantakar da ke tsakanin al’ada da addini, domin a cikin littafin an nuna cewar daya daga cikin addinin gargajiya na Hausawa shi ne Bori wato bautar iskokai. Bori tsohuwar al’ada ce w...