Skip to main content

HAKIMAN KATSINA

#MU SAN HAKIMAN MU!

👇
JERIN SUNAYEN HAKIMAN KATSINA AMMA BA ANYI BANE BISA DARAJAR GIRMA IN BANDA HAKIMAI HUDU NA FARKO

1. Kauran Katsina Hakimin Rimi Alhaji Nuhu Abdulkadir.

2. Galadiman Katsina Hakimin Malumfashi Hon Justice Mamman Nasir GCFR (Rtd).

3. Yandakan katsina Hakimin Dutsinma Alhaji Sada Muhammad Sada.

4.  Durbin Katsina Hakimin Jikamshi Alhaji Aminu Kabir Usman

5. Magajin Garin Katsina hakimin cikin Birni da Kewaye Alhaji Aminu Abdulmumin Kabir

6.  Sarkin Maskan Katsina Hakimin Funtua Alhaji Sambo Idris Sambo

7. Sarkin Musawa Hakimin Musawa Alhaji Muhammadu Gidado Usman Liman

8.  Kankiyan  Katsina Hakimin kankia Alhaji Musa Hassan Sada.

9.  Sarkin Sulluwan Katsina Hakimin kaita Alhaji Abdulkarim Kabir Usman.

10. Sarkin Shanun Katsina Hakimin Charanchi Alhaji Abashe  Abdulkadir.

11. Sarkin Yamman Katsina Hakimin Faskari Alhaji Tukur Usman Sa'idu.

12.  Sarkin Gabas din Katsina Hakimin Mani Alhaji Babani Isah Mani.

13. Sarkin Arewan Katsina Hakimin Jibia Alhaji Rabe Muhammad Rabiu.

14. Sarkin Kudun katsina Hakimin Danja Alhaji M T Bature.

15. Makaman Katsina Hakimin Bakori Alhaji Idris sule Idriss.

16. Sarkin Pauwan Katsina Hakimin Kankara Alhaji Yusuf Muhammad Lawal.

17.  Kogon Katsina Hakimin Sabua Engr  Bello Ibrahim.

18. Katukan Katsina Hakimin Dandume Alhaji Ja'faru Ibrahim.

19. Mallamawan Katsina Hakimin Batagarawa Alhaji Dikko Dalhatu.

20. Magajin Malan katsina Hakimin Dan musa Alhaji Dadda'u Yakubu.

21. Marusan katsina Hakimin Dutsi Alhaji Lawal Sani Dutsi.

22. Sarkin Ruman Katsina Hakimin Batsari Alhaji Tukur Mu'azu Ruma.

23. Maradin Katsina Hakimin Kurfi Alhaji Dr Ahmadu Kurfi.

24. Dan Yusufan Katsina Hakimin Bindawa Alhaji Muhammad Bello.

25. Bebejin Katsina Hakimin Kusada Alhaji Nuhu Yashe.

26. Fagachin Katsina Hakimin Matazu Alhaji Iro Mai kano.

27. Iyan Katsina Hakimin Mashi Alhaji Kabir Aminu Ibrahim.

28. Sarkin Fulanin Dambo Hakimin Ingawa Alhaji Abubakar Sule Abubakar.

29. Dan Galadiman Katsina Hakimin Kafur Alhaji Rabe Abdullahi.

30. Dan Barhin Din katsina Hakimin Doro.

31. Dan Madamin Katsina Hakimin Daddara Alhaji Usman Usman Nagogo.

32. Majidadin katsina Hakimin Tsageru Alhaji Garba Usman Nagogo.

33. Dan Isan Katsina Hakimin Rimaye Alhaji Yusuf Yakubu.

34. Sarkin Rafin Katsina Hakimin Mairuwa Alhaji Sani Idris Sambo.

35. Sarkin Fulanin Dangi Hakimin Yantumaki Alhaji Abubakar Atiku Maidabino.

36. Gado da Masun Katsina Hakimin Wagini Alhaji Dikko Muazu Ruma.

37. Danejin Katsina Hakimin Mahuta Alhaji Bello Abdulkadir Yarmama

38. Jarman Katsina Hakimin  Tsiga Group Captain Abubakar Bala (Rtd).

39. Kanwan Katsina Hakimin Ketare b Usman Bello.

40. Barden Katsina Hakimin Ajiwa Alhaji Bello kabir Usman.

41. Sarkin Kurayen Katsina Hakimin Kuraye Alhaji Abdullahi Ahmadu.

42. Gatarin Katsina Hakimin Zaka Alhaji Sani Zaka.

43. Yariman Katsina Hakimin Safana Alhaji Sada Rufa'i

44. Ubandoman Katsina Hakimin Yandoma Alhaji Muntari Dambo.

Comments

Popular posts from this blog

NAZARIN LITTAFIN KUL'BA NA 'BARNA NA UMARU 'DANJUMA KATSINA

NAZARIN DA SHARHIN LITTAFIN WASAN KWAIKWAYO (KULBA NA BARNA...) . -MAWALLAFI: UMARU DANJUMA KATSINA (KASAGI) SHEKARAR BUGAWA: 1979 SABUNTAWA: 1985; 2004; 2006; 2007 ISBN: 978-978-169-245-1 GABATARWA: 'KULBA NA BARNA...' littafin wasan kwaikwayo ne wanda ke kunshe da labarin wata yarinya 'yar makaranta mai suna Zaliha. Mahaifinta, Malam Bankami, mutumin kauye ne, ya rasu ya bar ta riko a hannun Kawunta da ke zaune a wani babban gari. Kawun nata, Malam Inuwa, ya so cika wasiyyar Mahaifin Zaliha na aurar da ita da zarar ta kammala makarantar firamare, har ba shi ma fatar ta ci jarabawar shiga babbar makaranta, kamar yadda yake cewa, . ''Ai da ma a cikin wasiyyar da ya bari, ya ce don Allah don Annabi idan Zaliha ta isa aure, in yi mata. Ya ce in aurar da ita ga duk wanda za ta samu zaman lafiya. Don haka ma nake fatar ka da Allah sa ta ci jarabawar nan ta zuwa makarantar 'yan mata.'' . Tuni dai har Malam Inuwa ya gama maganar auren Zaliha da iya...

ZANCEN KARSHE

AL'ADAR ZANCEN K'ARSHE    Masu iya magana kan ce 'darajar galan marfinsa haka kuma duk darajar girman tuwo sai an sa masa miya'. Sannan masana (addini da boko) sun tabbatar mana da cewar duk al'ummar da ta yada al'adarta, ko shakka babu wannan al'umma ta shiga garari (rud'ani).  'Zancen 'karshe' al'ada ce wadda ake gudanarwa a wani yanki na garin Katsina. Wannan al'adar na d'aya daga cikin al'adun auren Hausawa a wannan yanki. Ana gudanar da wannan al'ada ne a ranar daren daurin aure; wato ana gobe za a d'aura aure kenan, sannan ana yin zancen 'karshe ne da daddare. Yadda ake gudanar da wannan al'ada shi ne; A ranar daren daurin aure da safe zuwa marece za a sanar da abokanin ango inda za a had'u domin zancen 'karshe, ita ma ta 'bangaren amarya za a sanar da 'kawaye wurin da za a had'u domin zancen 'karshe. Kafin lokacin ya yi abokanin ango za su tanadi kayayyakin ma'kulashe kama...
TARIHIN SANA’AR BORI Tarihi ya nuna cewa shi dai bori shi ne imanin Bahaushe na asali, domin kuwa kowace al’umma idan aka bi tushe ko asalinta za a tarar tana da wata hanyar da ta ke bi  don yarda da wani abu mai girma wanda suka dogarar da rayuwarsu akansa. Tun can asali ma a kan samu wadansu al’ummomi da suke bautar gumaka ko iskoki ko taurari ko wuta da sauransu. Haka kuma tarihi ya nuna cewa kafin shigowar wasu bakin al’ummomi a kasar Hausa, Hausawa suna da addininsu na gargajiya.A sakamakon irin nazarce-nazarce da aka yi a baya dayawa daga cikin masana na nuna cewa tarihin bori shi ne addinin gargajiya na Hausawa kai har ma da wasu wadanda ba Hausawa ba. A wani bincike da na yi na samu wani littafi mai suna ‘Dangantakar Al’ada Da Addini’   wanda a cikin littafin aka nuna irin dangantakar da ke tsakanin al’ada da addini, domin a cikin littafin an nuna cewar daya daga cikin addinin gargajiya na Hausawa shi ne Bori wato bautar iskokai. Bori tsohuwar al’ada ce w...